Ana saran dan wasan gaban Manchester United Anthony Martial zai bar kungiyar ta Premier a matsayin dan wasa kyauta.
Martial, wanda a halin yanzu yana jinya, zai ga kwantiraginsa na yanzu ya kare a karshen kakar wasa ta bana.
Kuma a cewar kwararre a harkar kwallon kafa Fabrizio Romano, dan kasar Faransa ba zai kasance a Old Trafford a kakar wasa mai zuwa ba.
Romano ya wallafa a shafinsa na Twitter da safiyar Litinin cewa: “Anthony Martial zai bar Man United a karshen kakar wasa ta bana, babu shakka.
“Zai zabi zabin da ya fi so a matsayin kulob na gaba a cikin watanni masu zuwa, yanzu ya mai da hankali kan murmurewa.”
Martial ya kulla yarjejeniya da United a shekarar 2015 kan kudin farko na fam miliyan 36 da kuma fam miliyan 21.6 na yuwuwar biyan kari.
Wannan shi ne mafi girman kuɗin da aka biya wa matashi a tarihin ƙwallon ƙafa a lokacin.