Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya bukaci mahukunta a bangaren wasanni a Sifaniya da ma sauran kasashen Turai a kan su dakatar da yaduwar nuna wariya ko furta kalaman wariyar launin fata a filin wasa.
Shugaban ya yi wannan kiran ne bayan da aka nuna wa dan wasan kwallon kasarsa Vinicius Junior wariya a wasan da Valencia ta yi da Real Madrid a jiya Lahadi.
An dakatar da wasan a zagaye na biyu a yayin da kungiyar Real Madrid ta mayar da martani a kan abin da ya faru.
Alkalin wasa ya kori dan wasan na Real Madrid mai shekara 22 a minti na 97 a wasan da Valencia ta doke su 1-0, bayan rigima da ya nemi yi da Hugo Duro.
An dai rika rera kalaman wariyar launin fata a filin wasan.
Bayan wasan Vinicius ya bayyana gasar La Liga da cewa ta masu wariyar launin fata ce
A kakar wasanin bana an sha furta kalaman wariya ga Vinicius Junior, wanda ya girma a wani garin marassa karfi da ke wajen birnin Rio de Janeiro, na Brazil.