Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani jami’inta mai suna Koufr Basiru Ibrahim da ake zargin abokin aikinsa Sufeta Hussaini Sani ya harba a lokacin da suke kan hanyar su ta komawa wajen aiki a jihar Katsina.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da bindigar da ke hannun Hussaini ta harba kanta, inda ta samu marigayin a ciki kuma bayan kai shi asibiti ya rasu.
Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu sun ce a gefen titin kurnar Asabe da ke birnin Kano aka yi harbin.
Tuni rundunar ta ce ta kama dan sandan da ya yi harbin don gudanar da bincike a kan afkuwar lamarin.
Wannan ne dai karon farko a 2022 da wani dan sanda ya kashe abokin aikinsa a Kano, in da a 2021 ma aka samu wani dan sanda a jihar da ya harbe abokin aikinsa saboda ya yi masa dariya. A cewar BBC.


