Ana zaman dar-dar a yankin Umualumaku da ke karamar hukumar Ehime Mbano a jihar Imo, biyo bayan kashe jami’an tsaro da ba su wuce takwas ba da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi.
Wadanda suka mutun sun hada da sojoji, jami’an ‘yan sanda, da jami’an tsaron farin kaya na Najeriya.
Lamarin da ya afku a safiyar ranar Talata, ya haifar da fargaba, inda mazauna yankin suka kara tada jijiyoyin wuya.
Rahotanni sun ce an kai wa wasu motocin jami’an tsaro guda biyu hari tare da kona musu wuta.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa DAILY POST cewa an aike da karin tawaga zuwa wurin da lamarin ya faru a kokarin damke wadanda suka aikata laifin tare da kwato gawarwakin jami’an tsaron da suka mutu.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya nemi a ba shi lokaci domin samun cikakken bayani kan wannan mumunan lamarin.


