Shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya ce, labaran kanzon kurege na kara ingiza rikici a Najeriya, kuma sukan kara rura wutar rashin tsaro da yi wa kokarin gwamnati kafar angulu da kuma kara fusata yan kasa, tare da haifar da rashin yarda tsakanin al’umma da gwamnati.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake wani taron ilimantarwa na UNESCO game da kafofin yada labarai na duniya wanda zauren matasan Najeriya ke karbar bakunci.
Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari ya ce, samun bayanan da za a dogara a kansu kullum shi ne ya dda za a samu tsaftatattun bayanai, kuma babu abin da suke yi sai haifar da barazana a cikin al’umma.