An soma shari’ar wani mutum da ake zargi da yi wa abokiyar aikinsa fyaɗe a majalisar dokokin Australiya.
An soma shari’ar ce a kotun koli da ke Canberra.
Ana tuhumar Bruce Lehrmann, wani tsohon mai ba da shawara kan harkokin siyasa da cin zarafin Brittany Higgins, wata mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai awani ofishin minista cikin watan Maris ɗin 2019.
Mista Lehrmann dai ya musanta zarge-zargen.
Miss Higgins kuwa ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da ta ɗaɗɗaki barasa ta kuma shiga bacci mai nauyi.
A cewarta ta farka ne ta ga Mista Lehrmann yana amfani da ita duk da ta sha nuna masa ba ta so. Za a shafe fiye da wata guda ana shari’ar. In ji BBC.