Ana sa ran shugaba Bola Tinubu zai dawo Abuja ranar Lahadi bayan ziyarar aiki da ya yi a kasar Sin da kuma ziyararsa a Burtaniya.
A ranar 29 ga watan Agusta, Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Beijing na kasar Sin, amma ya zarce a Dubai, UAE.
Ya isa birnin Beijing a ranar 1 ga watan Satumba domin fara ziyarar aiki a kasar Sin.
Shugaban ya fara ziyarar aiki a ranar 2 ga watan Satumba, inda ya gana da shugaba Xi Jinping a babban dakin taron jama’a.
An yiwa shugaba Tinubu gaisuwar bindigu 21. Ya kuma duba masu gadin.
Wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar ta ce, “An sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda biyar tsakanin Najeriya da China a wajen taron.
“Shugaba Tinubu ya jagoranci tawagarsa zuwa wani zagaye na tattaunawa da firaministan kasar Sin Li Qiang washegari.”
A yammacin wannan rana, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun karbe shi a wajen liyafar maraba da nuna al’adun gargajiya a jajibirin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC).
Tinubu ya bar birnin Beijing zuwa Landan, inda ya shafe kwanaki.
A ranar Alhamis, ya gana da Sarki Charles na uku don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi.