Yayin da ake tunkarar shirye-shiryen fara aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya, maniyata na nuna damuwa kan yadda yanayin zafi ke ƙaruwa a birnin Makka da kewaye.
Hakan na zuwa ne yayin da dubun dubatar Musulmi ke ci gaba da kwarara zuwa birni mai tsarki, gabanin fara aikace-aikacen hajji a ranar Jumu’a.
Tuni dai hukumomin ƙasar Saudiyya, suka tanadi na’urorin da za su taimaka wa maniyyatan bana wajen rage zafin da suke fuskanta.
A kalla fiye da mutane miliyan 1.3 ne za su gabatar da aikin hajjin bana.