Dubban jama’a na ci gaba da taruwa a shirye-shiryen fara jana’izar Shugaba Ebrahim Raisi wanda rasu a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu tare da wasu mutum bakwai ciki har da ministan harkokin waje.
Za a fara jana’izar ne a yankin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar ta Iran inda hadarin jirgin na helikwafta ya faru ranar Lahadi.
Tuni dubban jama’a suka fara tururuwa a titinan birnin na Tabriz domin nuna alhininsu ga marigayi shugaban da sauran wadanda suka rasu.
Ana sa ran binne gawar Shugaba Raisi a mahaifarsa da ke Mashhad, jibi Alhamis.