fidelitybank

Ana fargabar Injiniyoyi 3 sun mutu a kamfanin BUA

Date:

Ana fargabar wasu Injiniyoyi 3 na kamfanin Siminti na BUA sun mutu bayan da wasu tankokin mai guda biyu suka fashe a masana’antarsu da ke Sokoto ranar Juma’a.

Bayanai sun nuna cewa, wasu ma’aikatan kamfanin uku sun samu raunuka, kuma an kai su asibiti domin yi musu magani.

An kuma tattaro cewa daya daga cikin tankunan na dauke da man Dizal yayin da daya kuma na dauke da bakin mai.
A cewar majiyar, ma’aikatan na aikin tankunan ne a lokacin da suka fashe da misalin karfe tara na safe.

Wata majiyar kuma ta bayyana cewa wani bangare na masana’antar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar kwanan nan, gobara ta lalata.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Sokoto Bello Baban Addini, ya ce, suna ci gaba da kokarin kashe gobarar.

Ya kara da cewa suna gudanar da bincike kan musabbabin fashewar, adadin wadanda suka mutu da kuma irin barnar da ya yi a masana’antar.

Hukumar gudanarwar kamfanin har yanzu ba ta mayar da martani ga ci gaban ba

vanguardnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp