Daliban Jami’ar Jihar Nasarawa, NSUK, sun mutu ranar Juma’a a garin Keffi, sakamakon turmutsitsin da ya faru a lokacin rabon tallafin shinkafa da gwamnatin jihar ta yi musu.
Lamarin ya faru ne a dandalin taro inda aka ajiye buhunan shinkafa ana jiran isowar Gwamna Abdullahi Sule domin fara rabon kayayyakin.
A cewar wani dalibin da lamarin ya faru a gaban idonsa, Moses Ajah, ya ce gungun daliban da ke dakon shiga dandalin sun ci karfin jami’an tsaro tare da kutsawa ta kofar da lamarin ya faru.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuka.
“Wasu daga cikin daliban sun yi ta kokawa da ‘yan sanda kan shinkafar, kuma da yawan daliban suka samu bayanai, lamarin ya lalace.
“A yayin da muke magana wasu daliban sun samu raunuka kuma suna karbar magani a makarantar,” NAN ta ruwaito yana cewa.
Ya ce wasu daliban ne suka dauko buhunan shinkafa suka garzaya dakunan kwanan dalibai da sauran wuraren zamansu duk da cewa gwamnan bai isa ba domin kaddamar da rabon.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an ga jami’an ‘yan sanda suna karbo kayan agaji daga daliban.
Da aka tuntubi Mista Abraham Ekpo, jami’in yada labarai da tsare-tsare na Jami’ar, ya ce yana sane da lamarin amma har yanzu bai samu cikakken bayani ba.


