Ana fargabar ‘yan sanda uku sun mutu bayan wata arangama da wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne a ranar Alhamis a birnin Benin.
Rahotanni na cewa rikicin ya faru ne da rana, jim kadan bayan dan takarar gwamnan jihar Edo na jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebolo da mataimakin gwamnan da aka dawo da su, Phillip Shaibu, sun bar filin jirgin saman Benin daga Abuja.
Yayin da wasu majiyoyi suka ce ‘yan sanda uku sun samu raunuka a harbin bindiga, wasu kuma sun ce ‘yan sanda uku ne suka rasa rayukansu a yayin arangamar.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor domin jin ta bakinsa, ya ce suma sun ji labarin a matsayin jita-jita, ya ce da wuri ne rundunar ta yi wani bayani a kai ba tare da bincike ba.
An bayyana cewa, ba a jima ba Okpebholo da Shaibu suka bar filin jirgin, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, a cikin wata motar Sienna da aka ajiye a kofar fita daga filin jirgin, sun harbe ayarin motocinsu.