Ƙwararru a fannin Kiwon Lafiyar Jama’a a jihar Kano, sun fara bayyana damuwa kan yiwuwar barazanar ɓarkewar cutar amai da gudawa da zazzabin cizon sauro a wasu daga cikin jihohin da ke arewacin kasar.
Gargaɗin na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun ambaliyar ruwa, sakamakon mamakon ruwa sama.
Ƙwararrun sun ce akwai matakai da dama da ya kamata a ce hukumomi sun ɗauka gabanin faduwar damunar bana, la’akari da hasashen masana da hukumomin kula da yanayi daban-daban suka bayar na fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu. In ji BBC.


