Cibiyar da ake tattara sakamakon zaben kasar Kenya da ke Nairobi, babban birnin kasar ta dauki harama a yayin da hukumar zaben kasar take kammala tsarin sanar da wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
A cewar BBC, abubuwa sun kankama a wurin da za a sanar da sakamakon zaben inda wakilan ‘yan takarar shugaban kasa da lauyoyi da kuma jami’an hukumar zabe suka dukufa wajen tantance takardun rubuta sakamakon zaben da aka aiko daga yuankuna daban-daban na kasar.
Ma’aikata suna can suna goge tebura da kujeru wadanda jami’ai suka yi amfani da su.
Kawo yanzu babu kwamishinonin zabe a wurin da za a sanar da zaben, amma rahotanni sun ce watakila suna can suna gudanar da taruka domin fitar da sanarwar karshe ta sakamakon zaben shugaban kasar.
Babban dakin da za a sanar da sakamakon zaben kasar kenya ya kwashe kwanaki da dama cike da hayaniyar jama’a, inda a wasu lokuta akan samu sabani game da tsarin tattara sakamakon zaben, sai dai yanzu abubuwa sun lafa.
An kara matakan tsaro a kofar shiga babban dakin tattara sakamakon zaben.
Kawo yanzu, Mataimakin shugaban kasa William Ruto yana gaban tsohon Firai Minista Raila Odinga – inda ya samu kashi 51% yayin da shi kuma Odinga ya samu kashi 48%, a cewar kafafen watsa labaran kasar.
Dole ne a ranar da sakamakon zaben zuwa ranar 16 ga watan Agusta, kamar yadda dokokin kasar Kenya suka bayyana.


