Kusan ya zama abin yayi kwana nan a Afirka – inda ake samun wasu ‘yan tsirarun sojoji da ke bayyana a Talabijin suna sanar da juyin-mulki.
A wannan lokaci maguɗin zaɗe shi ne dalilin da aka yi amfani da shi wajen kifar da gwamnatin Ali Bongo, shugaban ƙasar Gabon, sa’o’i bayan bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen kasar me cike da ce-ce-ku-ce. An haramtawa masu sa ido daga ketare da ‘yan jarida shiga ƙasar domin bada rahoton zaɓen.
A wani yanayi da aka saba ganin yada ake amfani da kuɗi wajen sayen magoya-baya, abu ne mai wahala a iya gane soyayyar gaskiya a wannan lokaci.
Amma a Gabon babu shaku abubuwa sun bambanta ganin cewa an gaji da ganin iyalan gidan Bongo da ke mulkin ƙasar tun 1967.
Kusan mulki ya zama wani abin gado ga wannan zuri’a abin da ya damu ‘yan kasar da dama. Mutane ba su ja kafa ba, wajen fantsama kan tittuna, cikin raha da farin ciki, yanayin da babu shaka ya nuna zakuwarsu ko gajiya da mulkin gida guda. Har yanzu dai babu alamar nuna turjiya.
Ga ƙasashen duniya, ciki harda Tarayyar Afirka, wannan yanayi abin damuwa ne. Faransa ta ruga wajen fitar da sanarwar alla-wadai.
Tasirinta a Afirka na fuskantar kalubale da barazana a shekarun baya-bayanan, sannan tana kiran a bari Ali Bongo ya kara wasu shekaru a mulki wanda ba lallai ya yi wa ‘yan kasar daɗi ba. In ji BBC.


