Rahotanni sun ruwaito cewa ana ci gaba da harbe-harben bindiga, tun bayan zaben kananan hukumomi a jihar Ribas da ya zo da rabuwar kawuna.
Akalla mutane biyar ne ake fargabar sun mutu a jiya Litinni, biyo bayan harbe-harben da ake zargi wasu ‘yan barandan siyasa suka yi a sakatariyar kananan hukumomi daban-daban na jihar Ribas.
Haka kuma ‘yan barandan sun fatattaki sabbin shugabannin wasu kananan hukumomin da aka rantsar daga ofishinsu, tare da yin ƙon-ƙone.
Alhaji Muhammad da ke hada-hada a jihar ta Rivers ya shaida wa BBC cewa ana zaman ɗar-ɗar a faɗin jihar, lamarin da ya sanya mutane suka ɗimauce saboda rashin tabbas na tsaron kansu da dukiyoyinsu, “Duk wanda zai yi iya yawo yanzu to ya saida ransa.”
Sai dai Yahya Wunti wani mazaunin jihar ya shaida wa BBC cewa a yankinsu an samu zaman lafiya, “Al’amurra sun dai-daita komai ya dawo dai-dai, babu abun da ke faruwa.”
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya umurci ƴan sanda da su samar da tsaro ga jami’an kananan hukumomin tare da dawo da zaman lafiya, da doka da oda cikin gaggawa.