Al’ummar jihar Edo a na ci gaba da kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen gwaman jihar da ke gudanar a yau Asabar.
Wakilin BBC da ke jihar ya ce an samu fitowar masu zaɓe musamman a mata a wasu rumfunan zaɓen.
Ma’aikatan hukumar zaɓen na amfani da na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS a lokacin zaɓen.
Tuni dai aka girke jami’an ‘yansanda a faɗin jihar domin tabbatar da tsaro a lokaci da kuma bayan zaɓen.