Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce, za a san makomar yankin Donbas da ke yammacin Ukriane, a yakin birnin Severodonetsk.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da gwabzawa mummunan fada a can, yayin da adadin wadanda suke rasa rai da jikkata ke karuwa a kowacce rana, sannan dakarun Rasha na kara dannawa cikin birnin.
Wakilin BBC ya ce karar da ke fita a yankin ta bambanta, ya yin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada, a makwannin da suka gabata lamura sun kara zafafa, yayin da bangarorin biyu ke cewa su na nasara, sai dai a bayyane ta ke sojin Rasha na gab da mamaye birnin.
Gwamnan yankin, Serhiy Haidai, ya ce a yanzu mayakan Ukraine wani dan bangare na wajen Severodonetsk kadai su ke iko da shi, wanda wata hanya ce da ta hada kudu masu gabashin Ukraine da suke kokarin karewa daga luguden wuta. In ji BBC.