Dubban ‘yan kasar Kenya sun taru a babban filin wasa na birnin Nairobi domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Kenya Mr. William Ruto.
Tun karfe 3 na dare jama’a suka fara isa filin wasan.
Jami’an tsaro sun rufe manyan hanyoyin birnin kuma an baza ‘yan sanda a harabar filin wasan da kuma a cikin birnin.
Ana sa ran akalla shugabannin kasa 20 ne za su halarci wannan bikin.
Yayin bikin shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta za mika kambun iko – wato wani takobi da kuma kundin tsarin mulkin kasar – ga sabon shugaban kasar William Ruto.
Tun da fari Mista Kenyatta ya ki taya zababben shugaban murnar lashe zaben shugaban kasar, amma a ranar Litinin ya sanar cewa a shirye yake ya tabbatar da an wanzar da zaman lumana a kasar kuma ya bukaci sabon shugaban da ya zama shugaban dukkan ‘yan kasar.