fidelitybank

Ana ƙoƙarin zaƙulo mutane 30 da ƙasa ta rufta da su a Neja

Date:

Mutum 30 ne ƙasa ta danne bayan wani ramin haƙar ma’adanai ya rufta a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta tabbatar da cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da aka ceto mutum shida waɗanda suka samu raunuka.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo da ke ƙaramar hukumar Shiroro, kuma ana ganin cewa mamakon ruwan sama da aka samu ne ya haifar da lamarin.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta Neja, Abdullahi Baba Arah ya tabbatar wa BBC a safiyar yau Laraba cewa ana wani yunƙuri na samar da iskar shaƙa ga mutanen da ke maƙale a ƙarƙashin ƙasa.

Neja na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya waɗanda ke ƙunshe da albarkatun ƙasa masu yawa, wadda kuma ke fama da matsalar tsaro.

A irin waɗannan yankuna akan samu wuraren haƙar ma’adanai da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba kuma ba a ɗaukan matakan kariya da suka kamata.

besda salary

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp