fidelitybank

Ana ƙoƙarin shafawa Manjo Janar Erema kashin kaji cewa ya sayi gida a Amurka da kuɗin sata – Sojoji

Date:

Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta lura cike da damuwa da kokarin wasu mutane na birkita tunanin jama’a da gangan, ta hanyar yunkurin shafa kashin kaji da jamhuru ga wani babban hafsanta, Manjo Janar Erema Akerejola, kan zargin sayen gida a Amurka da kudaden almudahanar kwangila.

Ta ce ba shakka, an sayi gidan da ake magana kansa a Amurka, amma bisa yarjejeniyar rancen gina gida da ake biya wata-wata, kuma har yanzu matar Manjo Janar Erema Akerejola wadda mazauniyar Amurka ce, tana ci gaba da biya.

Rundunar sojin Najeriya a sanarwar da daraktan hulda da jama’anta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce kokarin nuna cewa mai gidan asali ya/ta fito ne daga gidan talakawa, wani kokarin kunyata dukkan ‘yan Najeriya ne masu aiki tukuru, wadanda suka tabuka wani abin kirki a rayuwa.

Sanarwar ta ce muhimmin abu ne a lura cewa an nada Janar Erema Akerejola kan mukamin Babban Hafsan Tsara Dabarun Sufuri da Gyare-gyare na rundunar sojin Najeriya ne wata shida da ya wuce, gidan kuma da ake magana kansa, an mallake shi ne shekara 12 a baya.

Ta kalubalanci mutumin da ya buga labarin a jaridar Sahara Reporters ta intanet da cewa bai iya gabatar da wata shaida ba, in ban da kalmomin wata majiya da bai iya bayyana sunanta ba, wadda ga alama a cewar rundunar sojojin Najeriya na cike da hauci, idan ma akwai ta a zahiri.

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...
X whatsapp