Wata Kotu da ke Kubwa a Abuja, ta bayar da umarnin a tsare Abba Mohammed a gidan gyaran hali bisa zargin sata.
Alkalin kotun, Muhammad Wakili ya ba da umarnin, bayan Mohammed ya amsa laifin da ake zarginsa da shi.
Wakili, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba domin yanke hukunci.
‘Yan sandan dai sun tuhumi wanda ake tuhuma da laifin aikata laifuka da kuma sata.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, SP Babajide Olanipekun, ya shaida wa kotun cewa Mohammed ya shiga wani shago da ke kan titin Gado Nasko, Kubwa, Abuja, da fakewa da siyan bututun iskar gas a ranar 11 ga Satumba.
Olanipekun ya ce Mohammed ya saci kudi N23,500 daga hannun wani Uchenna Madugba, amma yayin da yake kokarin tserewa, an kama shi.
Lauyan mai shigar da kara ya ce an kwato kudaden ne daga hannun Mohammed, inda ya kara da cewa laifin ya saba wa sashi na 348 da 288 na kundin laifuffuka.
Sashi na 288 ya ce duk wanda ya yi sata za a yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai ko tara ko duka biyun. (NAN)