An yanke wa wasu tsofaffin shugabannin kungiyar Proud Boys masu ra’ayin rikau su biyu hukuncin dauri mai tsawo a gidan yari, sakamakon samun su da hannu a rikicin da ya faru a majalisar dokokin Amurka da ke birnin Washington a shekarar 2021.
An yanke wa Joe Biggs, tsohon sojan Amurka ne zaman kason shekara 17, yayin da Zachary Rehl kuma shekara 15.
Norman Pattis, wanda shi ne lauyan daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, Joe Biggs; ya ce sakamakon zaman bai yi kyau ba. Ya kara da cewa yanke musu hukuncin daurin shekara 17 da 15 ya yi yawa, mun dauka akwai sassaucin da za su samu kamar shekara 10.”
Dukkansu sun fashe da kuka tare da yin da na sanin abin da suka aikata.
Masu shigar da kara sun ce Biggs ya jagoranci far wa Capitol don murde nasarar da Joe Biden ya yi a zaben 2020.


