Gwamnatin tarraya ta kwaso ƙarin mutum 13 da suka tsere wa yaƙi a Sudan kuma suka maƙale a Saudiyya.
Mutanen sun sauka a filin jirgi na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a jiya Asabar bayan sun biyo jirgin Qatar Airways tare da taimakon hukumar ba da agaji ta National Emergency Management Agency (NEMA).
Jimillar adadin waɗanda gwamnatin Najeriyar ta kwashe daga Sudan ya zama 2,531 ke nan.
Tun a ranar 13 ga watan Mayu aka kammala kwashe ‘yan ƙasar 2,518 daga Port Sudan da kuma Masar.