A ranar Laraba ne kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Joseph Albasu Kunini ya yi murabus.
Nan take majalisar ta zabi dan majalisa mai wakiltar mazabar Zing, John Kizito Bonzina, a matsayin sabon shugaban majalisar.
An zabi Kunini ne a dandalin jamâiyyar Peoples Democratic Party a 2019.
Wasikarsa ta murabus da ya karanta a falon majalisar ta baiwa kowa mamaki domin babu wani salon fada tsakanin âyan majalisar.
âAikin murabus na ya kasance a kan kashin kaina. Ina mika godiyata ga âyan uwa masu girma bisa goyon baya da hadin kai da suka ba ni a lokacin da nake shugabantar wannan majalisa mai girma,â inji shi.
Bonzina, yayin da yake magana bayan hayewar sa a matsayin sabon shugaban majalisar, ya musanta zargin cewa âyan majalisar sun yi juyin mulki a fadar shugaban kasa domin tsige shugaban majalisar daga mukaminsa.
Yayin da yake neman goyon bayan takwarorinsa, ya yi alkawarin yin aiki ba dare ba rana domin ci gaban nasarorin da tsohon kakakin ya samu.