Mataimakin shugaban babban masallacin Legas, Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy, ya zama Baba Adinni na 14 na Legas.
Zamowar Alhaji Alabi-Macfoy a matsayin baba Addinin ya biyo bayan zaben da aka yi cikin lumana a ranar Laraba a babban masallacin Legas da ke unguwar Idumota.
Daga cikin mutane uku da suka nuna sha’awar wannan muƙamin, mutum biyu ne suka samu halartar tantancewar da aka yi, wato Alhaji Alabi-Macfoy da kuma Alhaji Jelili Animashaun.
Daya daga cikin ‘yan majalisar tafiyar da lamurran babban masallacin na Legas, Alhaji Fatai Dawodu, shi ne ya jagoranci kwamitin tantancewa na mutane 30.
Ƴan takarar biyu sun sha tambayoyi kafin ‘yan kwamitin suka fara kada kuri’a.
Alhaji Alabi-Macfoy ya yi nasara da kuri’u 22 yayin da Alhaji Animashaun ya samu kuri’u takwas.
Nasararsa a matsayin Baba Adinni, Cif Alabi-Macfroy zai gaji Sheikh AbdulHafeez Abou, wanda ya rasu a ranar 9 ga watan Janairu yana da shekara 101.