An zabi dan wasan gaba na Najeriya, Victor Boniface a matsayin gwarzon dan wasan Bundesliga na watan Agusta.
Boniface zai fafata da ‘yan wasan Bayern Munich biyu, Harry Kane da Alphonse Davies, da kuma dan wasan Wolfsburg, Jonas Wind.
Kevin Behrens na Union Berlin da mai tsaron bayan RB Leipzig Benjamin Henrichs don kyautar.
Dan wasan mai shekaru 22 ya zura kwallaye biyu kuma ya taimaka a wasanni biyu da ya buga wa Leverkusen a watan Agusta.
Har ila yau, dan wasan yana cikin masu neman lashe kyautar gwarzon shekara na Bundesliga.
Golan haifaffen Najeriya, Noah Atubolu da Xavi Simons na RB Leipzig su ne sauran ‘yan wasan da aka zaba don wannan kyautar.
Ya zuwa yanzu Boniface ya zura kwallaye hudu kuma ya taimaka daya a wasanni uku da ya buga wa Die Werkself.
Ya haɗu da ƙungiyar Xabi Alonso daga ƙungiyar Belgian Pro League, Union St Gilloise wannan bazara.


