Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya isa sansanin Jabalia, inda hari ya kashe gomman Falasɗinawa.
Rahoton da yake bayarwa shi ne cewa an zaƙulo gawar mutum 47 zuwa yanzu.
Mazaunin wurin Ragheb Aqal ya ce sun ji wani abu mai kama da “girgizar ƙasa” ya afka wa sansanin.