An zaƙulo aƙalla gawarwakin mutum 11 daga cikin wata bola a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya, bayan da mazauna yankin suka ankarar da hukumomi.
Shaidu sun ce da yawa daga cikin gawarwakin na mata ne, yayin da ka daddatsa wasu daga ciki.
Kawo yanzu dai ba san abin da ya haddasa mutuwar mutanen ba, yayin da rahotonni ke nuna cewa akwai wasu ƙarin gwarwakin.
‘Yansanda sun ce an zaƙulo gawarwakin mutum shida – dukansu mata – da aka yayyaka wasu sassan jikinsu, bayan da suka soma ruɓewa.
Jami’an tsaro sun killace wurin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.


