Shugaban ƙasar Saliyo Julius Maada Bio, ya ce, boren kin jinin gwamnati da aka yi a ƙasar cikin wannan mako wani yunkuri ne na hamɓarar da gwamnatinsa.
Lokacin da ya ke jawabi a kafar talabijin ta kasar, ya ce gwamnati ta yi kokari sosai wajen yaki da tsadar rayuwa. In ji BBC.
‘Yansanda shidda da wasu fararen hula ne aka kashe lokacin zanga-zangar a ranar Laraba a lokacin da jami’an tsaro suka yi amfani da barkono mai sa hawaye da bindiga wajen tarwatsa masu zanga-zangar a Freetown babban birnin kasar.
Sama da mutum 100 ne aka kama tare da sanya dokar hana fita a cikin dare.


