Tsohon ɗan ƙwallon Najeriya, Tijjani Babangida ya ce matarsa, Maryam Waziri ta rasa idonta guda ɗaya kuma an yi mata tiyatar gyaran fuska a Netherlands.
A ranar 9 ga watan Mayu ne wani mummunan hatsarin mota ya rutsa da Babangida da iyalansa ciki har da ƙaninsa da matarsa da ɗansa mai shekara ɗaya da rabi, a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Cikin wata hira da ya yi da tsohuwar ƙungiyarsa ta Ajax Amsterdam a Netherland, Babangida ya ce damuwar da ya shiga ba za ta taɓa gushewa ba.
Maryam Waziri wadda tauraruwa ce a masana’atar shirya fina-finai ta Kannywood, ta auri tsohon ɗan ƙwallon ne a watan Nuwamban 2021.
Ƙaninsa Ibrahim Babangida ya mutu nan take bayan hatsarin, yayin da ƙaramin ɗansa, mai suna Fadil ya rasu kwanaki bayan hatsarin, sannan mai aikin gidansu ta samu karaya a ƙafa.
Tsohon ɗan wasan na Najeriya ya c,e shi ya ji raunuka a ƙafarsa a lokacin hatsarin, don haka ne ya ƙudiri aniyar taimaka wa matar tasa inda ya tafi Netherlands domin ta samu cikakkiyar kulawa.
Ya kuma ce sakamakon yanayin da matar tasa ta shiga ta manta komai na rayuwarta.
“Bayan shafe wata uku a nan Netherlands, na faɗa mata cewa hatsarin ya rutsa da ƙaramin ɗanmu. Daga nan sai ta fara tambayata wai ya sunansa. Ba ta iya tuna komai”, in ji shi.
Babangida ya kuma yaba da irin gudunmowar da abokansa na ƙwallon ƙafa suka ba shi a ƙasar ta Netherlands.
Ya ce sun taimake shi da duk abin d ake buƙata, kuma sun fara gangamin tara masa kuɗi domin daukar ɗawainiyar jinyar matar tasa, wadda ya ce za ta kwashe shekara guda ana yi mata aiki a asibitin.