Wata babbar kotun jihar Jigawa da ke zamanta a Birnin Kudu a ranar Alhamis, ta yankewa wani matashi dan shekara 25, Israfilu Sagiru da ke kauyen Zarena da ke karamar hukumar Birnin Kudu hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin fyade.
An fara gurfanar da wanda ake tuhumar ne a ranar 5 ga Satumba, 2021, a gaban babbar kotu a kan tuhumar aikata laifuka biyu na fyade da ake yi masa na lalata da almajirai biyu masu shekaru 11 da 12, bisa zargin ba su sabbin tufafi.
Domin tabbatar da karar, mai gabatar da kara ya kira shaidu uku, inda ya gabatar da bayanan ikirari na wanda ake kara da kuma shaidar jarrabawar binciken shari’a.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Musa Ubale ya ce masu gabatar da kara daga ma’aikatar shari’a ta jihar, sun tabbatar da dukkanin abubuwan da ke tattare da fyade.
Ya ce laifin ya sabawa sashe na 3 (1) (e) na dokar hana cin zarafin mutane (VAPP) mai lamba 02, 2021.
Don haka mai shari’a Ubale ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin rai da rai.