Kotun Kiyaye cin zarafi da laifukan kiyaye Hakkin Jinsi a jihar Legas, ta yanke wa wani malamin Islamiyya, hukuncin daurin rai da rai, bisa laifin lalata da ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara takwas.
Mai shari’a Ramon Oshodi ya yanke wa Isa Mustapha hukuncin ne bayan mai shigar da kara ya gabatar da shaidu hudu da suka tabbatar da laifin da ya aikata.
Sai dai wanda ake tuhumar, mai shekara 50, ya bayar da shaida domin kare kansa.
Kotun ta amince da hujjojin mai kara a kan wanda ake tuhuma.
Aikata fyade dai ya saba wa sashe na 137 na dokoar manyan laifuka a jihar Legas na 2015.