A safiyar Lahadi an yi wa lambar wayar Gwamnan Jihar Kuros Riba, Bassey Otu, kutse tare da roƙon kuɗi daga wajen manyan mutane.
Sanarwa daga babban sakataren yada labarai na gwamnan, Emmanuel Ogbeche, ya ce masu laifin sun aike da sakwannin da ba a san ko su waye ba da ake zargin gwamna Bassey Otu na neman taimakon kudi.
Sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da irin wadannan sakonni.
“Jama’a na jin dadin yin watsi da duk wani sako da ake cewa daga Gwamna.
“Masu aikata laifukan fasahar zamani sun karya daya daga cikin lambobin wayar Gwamnan a safiyar Lahadi, 11 ga Fabrairu, 2024.
“Masu kutse sun ci gaba da yin amfani da lambar da suka karya don ci gaba da munanan ayyukan su domin yin zamba ga mutanen da ba su ji ba gani. Don Allah, kada ku fada cikin irin wannan yunƙurin yaudara.”
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa an tsare lambar da aka yi kutse, kuma jami’an tsaro da abin ya shafa na kokarin kamo wadanda suka aikata wannan mugunyar aikin.