Babban alkalin jihar Zamfara, Mai shari’a Kulu Aliyu, ya yi wa fursunoni talatin afuwa ba tare da wani sharadi ba.
Mai shari’a Aliyu ya gargadi fursunonin da aka yi wa afuwa da su kaurace wa duk wani nau’in laifuka domin su zama masu amfani a cikin al’umma.
An sako fursunonin ne a babban gidan gyaran hali na Gusau.
Fursunonin da aka saki sun hada da wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, da kuma wadanda aka yanke wa hukunci kan laifuka daban-daban ko kuma masu jiran shari’a.
Daraktar kara ta jihar Barista Aisha Jibril ta ce babban alkalin ya gargadi fursunonin da aka yi wa afuwa da su canja halayensu.