Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya bayyana cewa an yi masa tiyata a hannu.
Musa ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Ya godewa Allah da ya yi nasarar yi masa tiyatar da aka yi masa a hannun hagu sannan ya kara da cewa karamar tiyata ce.
“Ina so in mika godiyata ga Allah da ya yi nasarar yi min tiyata a hannuna na hagu.
“Kamar yadda muka sani, babu aikin tiyata da ya yi ƙanƙanta, don haka ina godiya ga ƙwararrun likitocin da aka ba ni aikin da suka yi sosai.
“Har ila yau, a gare ku duka, don saƙonninku, addu’o’inku da kalmomin ƙarfafawa. Ina fatan zan dawo fagen daga nan ba da dadewa ba da karfi da kwarin gwiwa.” ya rubuta.