Shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Ribas, Sim Fubara, Edison Ehie, ya bayyana cewa an yi masa tayin kudi domin tsige gwamnan.
Sai dai Ehie ya bayyana cewa ya ki karbar kudin da aka yi masa tayin tsige Fubara.
Shugaban ma’aikatan wanda bai bayyana sunayen wadanda suka yi masa kudi ba, ya yi magana ne a yankin Ahoada ta Gabas na jihar Ribas a karshen mako.
A cewar Ehie: “Sun gayyace ni, danka, domin in tsige gwamna, kuma na fada musu karara, ba ni da sha’awa.
“Sun ba ni duk kuɗin da aka ɓoye a baya, wanda na ƙi. Kuma saboda na ki, sai suka hada baki suka ce ana nemana.”
A shekarar 2023, ‘yan sanda sun bayyana cewa suna neman tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar bisa zargin mamaye majalisar dokokin jihar.
A watan Oktoban shekarar 2023, fashewar wani abu ya rutsa da ginin majalisar dokokin jihar a daidai lokacin da rahotanni ke cewa ‘yan majalisar na yunkurin tsige Fubara.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan majalisar karkashin jagorancin Martin Amaewhule sun shigar da kara kan Ehie ga hukumar ‘yan sandan jihar Ribas dangane da mamaye majalisar dokokin jihar Ribas da kone-kone da wasu ‘yan daba da ba a tantance ba.