An yi jana’izar ‘yar Kannywood, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso a gidan Sarkin Kano.
Dubundubatar mutane ne su ka halarci jana’izar tare da manyan mutane da al’ummar jihar Kano.
Kafin rasuwar ta dai ta bayyana a shafin ta na sada zumunta ta na cewa, ta saita abin hangen nesanta, domin ganin watan Sallar Idi.