Tsohon Ministan kwadago na kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP Musa gwadabe ya rasu.
Musa Gwadabe ya rasu a ranar Laraba a wani asibiti a kano, ya mutu yana da shekara 87 bayan fama da goguwar rashin lafiya.
Musa Gwadabe ya taɓa zama shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kano.
An shirya gabatar da jana’izarsa ne a titin Ado Makoɗa da ke Kano da misalin ƙarfe 2 na ranar.
Ya mutu ya bar mata biyu da yara 11 da kuma jikoki.