A yau aka gudanar da jana’izar Babban Sakataren Kungiyar OPEC, Dakta Muhammad Sanusi Barkindo wanda ya rasu a ranar Talata da dare.
An gudanar da jana’izar ne a birnin Yola da ke Jihar Adamawa.
Barkindo ya mutu ne a ranar Talata, bayan ya kammala ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.