Dubban mutane cikinsu har da shugabannin ƙasashe ne za su halarci jana’izar tsohon firaministan Japan Shinzo Abe da ya mutu bayan kisan gillar da aka yi masa cikin watan Yuli.
An tsananta matakan tsaro a Tokyo, babban birnin ƙasar, inda za a yi jana’izar.
Daga cikin fitattun mutanen da suka halarci wurin akwai Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris da Firaministan Indiya, Narendra Modi da takwaransa na Australiya Anthony Albanese.
Wakilin BBC ya ce labari ya bambanta a Tokyo inda kashi sittin na al’umma ke cewa ba su goyi bayan yi tsohon firaministan na Japan jana’izar ban girma ba.