Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta gabatar da wasu da ake zargi da ƙoƙarin haifar da tashin-tashina a yayin da ake aikin tattara sakamakon zaɓe a jihar.
Yan sandan sun ce ɓata-garin sun yi yunƙurin ƙona ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC a jihar.
A cewar rundunar, an samu mutanen da yunƙurin satar akwatin zaɓe da kuma sayen ƙuri’u.