Gwamnatin jihar Legas, ta wallafa sunayen wasu mutum uku da aka samu da laifukan fyaɗe a jihar.
Hukumar Yaƙi da Laifukan cin Zarafi ta jihar ce ta wallafa sunayen mutanen uku a shafinta na Tuwita
Hukumar ta wallafa sunaye da hotunan mutanen tare da irin nau’in laifukan da suka aikata da irin hukuncin da kotu ta yanke musu.
Ɗaya daga cikinsu mai suna Idowu Daniel, an same shi da laifin cin zarafi ta hanyar lalata, inda kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai.
Na biyun mai suna Moses Olawale wanda aka samu da laifin lalata ƙaramar yarinya, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekarar 37 a gidan yarin.
Sai kuma Akin Isaac, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 21 bayan da aka same shi da laifin fyaɗen.
Hukumar da ke Yaƙi da laifukan cin zarafi ta jihar ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su riƙa kai masu aikata irin wannan laifi gaban kotu don su girbi abin da suka shuka.
“Mu ci gaba da nema wa kanmu da waɗada aka ɓata wa rayuwa adalci a gaban kotuna,” in ji hukumar.
A watan Mayun shekarar 2022 ne hukumar ta bayyana aniyarta ta fara wallafa sunaye da hotunan masu aikata laifukan cin zarafi a shafukanta.