fidelitybank

An yi garkuwa da yara 39 a gona cikin jihar Katsina

Date:

A kalla yara 39 ‘yan bindiga suka sace a wata gona a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina wanda iyayen yaran suk roki gwamnati da ta kawo musu dauki.

‘Yan fashin, a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda wata majiya ta bayyana, da yawansu sun mamaye gonar da yaran ke aiki.

A cewar majiyar, al’ummar Mairuwa ne suka fi fuskantar hare-haren ‘yan bindigar. Ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun fara harbe-harbe kai-tsaye a lokacin da (’yan bindiga) suka kewaye gonar.

Majiyar ta kara da cewa an biya ‘yan fashin Naira miliyan 1 ne a matsayin haraji kafin wani wakilin gonar ya tara yaran, inda ya bayyana cewa galibin manya da ke aiki a gonar tare da yaran sun samu tserewa a lokacin harin.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Sun bukaci mai shi N3m domin ya samu damar girbin amfanin gonarsa, ya ba su Naira miliyan 1 a matsayin biyansu, sannan ya yanke shawarar fara aikin kafin su kammala kudin, amma abin takaici ‘yan fashin ba su amince da hakan ba. A kauyenmu mairuwa, kadai muna da mutum 33 daga cikin wadanda abin ya shafa ciki har da ‘yan mata da za a yi musu aure.”

Ya bayyana cewa mai gonar dan Funtuwa ne, amma wakilinsa yana zaune a kauyen Mairuwa, inda ya ce a yayin da yake magana ‘yan bindigar sun yi amfani da wayar daya daga cikin wadanda abin ya shafa suka kira suna neman kudin fansa naira miliyan 30.

Ya kara da cewa su (’yan fashi) sun ce sun je gonar ne domin su sace mai gidan ko kuma wakilinsa, inda ya jaddada cewa tun da ba su iya haduwa da ko wannensu ba, sai suka yanke shawarar yin garkuwa da wadanda suke yi musu aiki.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya tabbatar da cewa akwai ci gaba da kokarin da ‘yan sandan ke yi na ceto wadanda lamarin ya shafa tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro.

An kuma tattaro cewa shida daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun sami ‘yanci ranar Talata.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hogan ya mutu bisa cutar gazawar koda

An bayyana cikakkun bayanai game da mutuwar ɗan wasan...

Sojoji sun kashe rikaken dan Bindiga Dan Dari Biyar a Sokoto

Dakarun Operation FANSAR YANMA sun yi nasarar fatattakar wani...

An kashe utane 30 a yakin Thailand da Cambodia

An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka...

Ba mu ƙayyade shekarun shiga ƙaramar sakandare JSS1 – Ma’aikatar Ilimi

Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu...

Ido da Ido na ga yadda Sojojin Isra’ila ke kashe Falasdinawa – Tsohon Sojin Amurka

Wani tsohon sojan Amurk ya ce, ya ga yadda...

‘Yan majalisar Birtaniya 220 na neman ƙasar ta amice da ƙasar Falasɗinu

'Yan majalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta...

Buhari yaki karbar kyautar Agogon lu’u-lu’u da jirgin sama – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

An kama wanda ya kashe tsohuwar Matarsa a Jigawa

Ƴansandan Jihar Jigawa sun ce, sun kama wani mutum...

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan Kwankwaso

Fadar shugaban kasa, ta mayar wa tsohon gwamnan Kano...

Barau FC ta naɗa Ladan Bosso sabon kocinta

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da...

Am fara dawo da ‘yan Najeriya daga Afrika ta Tsakiya

Hukumomi a Najeriya sun ce, sun fara ƙoƙarin mayar...

G-Fresh da Hamisu Breaker sun samu gurbi kurkuku bayan sun watsa Naira

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ɗaure shahararrun...
X whatsapp