Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da wani Dakta Mansur Mohammed a jihar Zamfara.
Rahotonni na cewa, an yi garkuwa da jami’an lafiya da wasu da har yanzu ba a tantance adadinsu ba a hanyar Dansadau zuwa Magami a ranar Asabar da ta gabata, 25 ga watan Yuni, 2022.
Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar ta tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Talata.
Mansur shine Darakta Janar na Babban Asibitin Dansadau.
Da yake bayar da rahoton sace shi, NMA ta yi fatali da yanayin tsaro a jihar, inda ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi da su tashi tsaye wajen shawo kan matsalolin da ke damun kasar nan.
Asibitin kamar yadda Daily Post ta ruwaito, ya tabbatar da cewa, an kuma yi garkuwa da fasinjoji da dama a aikin.
Sai dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar dangane da lamarin.
A halin da ake ciki kuma, a ranar Talata ne gwamnatin jihar Zamfara ta fitar da sharuddan da ya kamata jama’a su samu damar mallakar bindigogi a jihar.