Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Ukum a jihar Benue, Rabaran Gideon Haanongon.
An tattaro cewa an yi garkuwa da Haanongon tare da mai taimaka masa kan harkokin mulki, Silas Yuhwam, direbansa da sanyin safiyar Asabar.
Sakataren Majalisar, Jonathan Modi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Modi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar a Anyagba, Tongov, cikin karamar hukumar Katsina Ala da misalin karfe 6:30 na safe.
Modi ya ce “An sace shugaban ne tare da jami’an sa, PA, da direban sa a hanyarsu ta zuwa halartar jana’izar babban sarkin LG, Ter Katsina Ala, HRH Cif Fezaanga Wombo,” in ji Modi a cikin sanarwar.
Modi ya kuma shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka yayin da ake daukar matakan tabbatar da cewa shugaban ya dawo da ‘yancinsa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai ba ta amsa tambayoyi kan lamarin ba.