Rahotanni daga jihar Taraba na cewa an sace mutum 21 har da sarki mai daraja ta uku na al’ummar Pupule, Alhaji Umaru Nyala a ƙaramar hukumar Yorro da ke jihar.
Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da su bayan da suka mamaye ƙauyen cikin dare inda suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi a sassa daban-daban na ƙauyen.
Wani shaida da ya yi hira da gidan Talabijin na Channels ya ce cikin mutum 22 da aka sace, har da wata mai juna biyu, da wasu ƴan gida ɗaya da kuma ɗan sarkin da dogarin sarkin.
Wannan ne karo na uku da ake sace mutane don neman kuɗin fansa a ƙauyen cikin ƙasa da wata shida kuma ba a taɓa cafke waɗanda ake zargi ba.
Shaidu sun kuma ce a yanzu, mutanen ƙauyen na zama cikin zullumi yayin da wasu kuma ke tserewa.
Har yanzu ƴan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba inda suka ce sun aike tawagar jami’ansu zuwa wajen domin gudanar da bincike.


