A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani masallaci da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, tare da yin garkuwa da wasu masu ibada.
An gano cewa an kai harin ne a lokacin da Musulman muminai ke sallar jam’i, Tahajjud.
Rahotanni na cewa, kawo yanzu ba a sanar da mutane nawa ne aka yi garkuwa da su ba a jihar.