Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida a garin Dutsinma da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.
Wata majiya ta shaidawa DAILY POST cewa, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa ‘yan uwan Umar Tafa ne, dan takarar gwamna.
Majiyar ta bayyana cewa, wadanda abin ya shafa baki ne da suka zo aure, an yi garkuwa da su kusa da gidan wani fitaccen dan siyasar da ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben fidda gwanin da ya gabata.
A cewar majiyar, matar da aka yi garkuwa da ‘ya’yanta akasari ‘yar uwar dan siyasar ce (Tata), wadda ta bayyana cewa, yadda maharan suka shiga gidan kai tsaye suka yi awon gaba da matan, abin mamaki ne.
Ya kara da cewa tun farko ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mutane 9 a Unguwar Kudu kwatas din garin amma daga baya suka sako mutane uku.
Majiyar ta ce, “Sun yi watsi da wata tsohuwa wadda ba za ta iya tafiya ba, tare da wani karamin yaro da ke ci gaba da kuka.”
Ya kara da cewa akwai lokacin da ‘yan fashin suka zo Dutsinma kwana hudu a jere suna garkuwa da mutane, inda ya ce lamarin ya kara ta’azzara kuma mun damu matuka.
Kakakin ‘yan sandan SP Gambo, bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, har ya zuwa lokacin da ake gabatar da rahoton.


