fidelitybank

An yi garkuwa da mutane 2,270 a Najeriya cikin kankanin lokaci – Rahoto

Date:

Wani rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Consulting da ke Abuja, ya fitar a makon nan ya nuna yadda ‘yan Najeriya 2,200 sannan an yi garkuwa da mutum 2,270 sakamakon matsalolin tsaro da ya hada da hare-hare ‘yan ta’adda da masu satar jama’a da kuma dakarun tsaro na gwamnati da na sa-kai.

Shugaban kamfanin, Malam Kabiru Adamu ya shaida wa BBC cewa kaso fiye da 90 na alkaluman na mace-macen da sace-sacen duka a arewacin Najeriya musamman arewa maso yammaci.

Ya kara da cewa a watan janairun wannan shekarar mun samu mutum fiye da 1000 da aka kashe, inda a watan biyu kuma aka samu fiye da 700 sannan a Maris din da ya gabata aka samu fiye da 800.

“Mun sami wadanda suka mutum mutum 855 a watan farko, a watan biyu kuma 747 ka ga kenan an samu karin 8.71 a cikin 100. Ka ga kenan mun samu mutum dubu biyu da dan wani abu a kai kenan.”

Dangane kuma da wadanda aka yi garkuwa da su Malam Kabiru ya ce “idan kuma ka zo batun garkuwa domin kudin fansa mun samu mutum 2270.”

To sai dai ya bayar da hanyoyin da idan aka bi su to za a kai ga gaci.

“Dole ne a samu hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnoni musamman na arewa.” In ji Malam Kabiru

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp